2 Agusta 2014 - 10:46
Sojin Iraki Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Da'esh Da Dama A Arewacin Kasar

Sojojin Iraki sun hallaka 'yan ta'addar Da'esh da dama a arewacin kasar. A wani farmaki da suka kai jiya juma'a Sojojin sun hallaka 'yan ta'addar Da'esh da dama tare da jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu. Tashar telbijin ta Press Tv wacce ke watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa wannan farmaki na a matsayin mayar da martani kan 'yan ta'addan na da'esh bayan sun kai hari kan wata matatar Men fetur a arewacin kasar.

Wannan Matatar Men wacce ke da nisan kilometa 200 daga arewacin Bagdaza ta zama wani fagen  yaki tsakanin Sojojin Iraki da kuma 'yan ta'addan Da'esh. 

Rikici a kasar ta Iraki yayi kamari ne bayan da kungiyar 'yan ta'adda na da'esh ta mayaye Garin Mosul da kuma Takrit mai nisan kilometa 140 a arewa maso yammacin Bagdaza.

Wannan rikici dai yayi sanadiyar raba Mutane fiye da million gida da mahalinsu kamar yadda MDD ta sanar da

Piraministan kasar Iraki Nuri Maliki ya daura alhakin ta'addancin dake faruwa a kasarsa kan kasashen Qatar da Saudiyyar sannan yayi kakkausar suka ga masarautar Saudiyyar wacce take a matsayin kasa ta farko mai taimakawa ta'addanci a kasashen musulmi domin kare  haramcecciyar kasar Isra'ila. ABNA